Ba-saban-ba: Bankunan Najeriya sun amince da hutun maza idan iyalinsu ta haihu

Ba-saban-ba: Bankunan Najeriya sun amince da hutun maza idan iyalinsu ta haihu

- Wata Banki ta bayar da sanarwan sabon tsarin bawa maza hutun raino na sati daya idan iyalan su sun haihu

- An fito da tsarin bayar da hutun ne domin mazajen su taimaka ma matan na su kuma su baiwa jariran na su kulawa mai kyau

- A karkashin tsarin, ma'aikata mata za su sami hutun watanni 3 ne tare da albashin su kamar yadda suka saba karba

Daya daga cikin manyan Bankunan Najeriya ta shawarci ma'aikata maza da mata da ke Bankin su rungumi sabon dokar bawa ma'aikatar hutun raino idan sun sami haihuwa ba tare an cire musu ko sisi a albashin su ba.

Maza da ke aiki a Bankuna za su fara samun hutu idan yalin su ta haihu
Maza da ke aiki a Bankuna za su fara samun hutu idan yalin su ta haihu

Bankin ta yi ta yi wannan kirar ne ranar Laraba a garin Legas, inda ta ce sabon tsarin da ya fara aiki daga watan Janairun wannan shekarar alama ne da nuna cewa Bankin na tafiya da kowa. Sanarwan kuma ta ce sabbi ta tsaffin ma'aikata duk za su iya morar garabasar.

DUBA WANNAN: Adadin yaran Najeriya marasa zuwa makaranta ya ragu zuwa 8.6% - Ministan Ilimi

Bankin ta kara da cewa wannan shine karo na farko da aka fara tsarin a Bankunan Najeriya, hutun rainon da za'a bayar na sati daya ga maza da mata wanda suka sami haihuwa ba zai sa ma'aikatan su rasa wani abu cikin albashin su ba.

A cewar Bankin, wannan hutun zai bawa iyaye mazan lokaci da za su bawa jariran su kulawa ingantaciya kuma su taimaka wa matan na su da raino. A cikin tsarin, ma'aikata mata za su sami hutun watanni 3 ne ba tare da albashin su ya yi ciwon kai ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel