Yar-tsana don saduwa: Lamarin ya rikita samari, ya kuma taada kishin mata
- An samar da bebin roba don biyan bukatar samari da ma 'yan mata
- Yar tsanar na aiki da batir, wasunsu ma suna rawa da magana
- Akwai mata akwai maza, akwai yara akwai manya, akwai turawa akwai bakaken fata
Zamani ina zaka damu! A wannan shekaru dai sabon salo a kasashen duniya shine na samar da bebin roba masu aiki da batura domin biya wa wadanda basu da iyali bukata ta sha'awa. Ana sayar da bebin robar ne dala dubu biyu, kusan naira 700,000 kenan.
Ita dai bebin robar akwai fara akwai baka, akwai ma masu rawa da duk wana siga ta motsa shawa'a, kuma a kowacce kasa ana iya oda a samu. Sai dai kuma al'adu a kasashen musulmi da ma na masu ra'ayin mazan jiya ba lallai su bari ba.
Akwai dai batu na abin-da-hannun daman-ka ya mallaka, ko bebin roba zata iya shiga wannan layin, sai anyi fatawa da fashin baki sannan zamu gane.
DUBA WANNAN: Buhari bai gayyaci Tinubu dinar jiya ba, me yayi zafi ne?
A yanzu dai wasu matan Najeriya sun bazama shafukan sada zumunta na facebook suna baza ra'ayoyinsu, suna cewa ragwancin maza ne a ce sun koma bin roba saboda gudun saya wa mace kayan shafe-shafe da na kwalam.
Su kuwa samari sarakan zumudi, sun ce sun huta da fada, da list na kayan saye, da sayan katin waya, da ma kuma tsoron ko ana yaudararsu ne.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng