Babu yadda za mu yi da berayen da ke cikin Aso Villa – Jalal Arabi
- Wani Jami’in Gwamnati yayi karin haske kan berayen da ke Aso Villa
- Jalal Arabi yace Garin Abuja na kan tudu ne shiyasa ya zama matattara
- Kwanakin baya dai beraye su ka hana Shugaban kasa Buhari aiki a ofis
Mun samu labari cewa wani babban Jami’in Gwamnatin Tarayya ya bayyana abin da ya sa ake fama da beraye da jaba a ofishin Shugaban kasa a Fadar Aso Villa da ke Birnin Tarayya yayin da ya gana da ‘Yan Majalisar Tarayya.
Jalal Arabi wanda Sakataren din-din-din ne a fadar Shugaban kasar ya tabbatar da cewa yanayin Garin Abuja ne ya sa dole ayi ta fama da beraye. Arabi yace asalin Abuja tana kan tudu ne da tsauni shi ya sa beraye su ka cika garin.
KU KARANTA: Nade-naden Shugaba Buhari sun bar baya da kura
Babban Jami’in Gwamnatin ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyi kan kasafin kudin bana a gaban Sanatocin kasar. Wani Sanata ya nemi jin ta bakin babban Jami’in ko sun shiryawa yin feshi a Fadar Shugaban kasar.
Arabi yace kwari da sauran su ba su rasa abin ci a Birnin Tarayyan. Bayan nan kuma ya bayyana cewa an ware kudi domin gyara asibitin fadar Shugaban kasa wanda kwanaki Uwargidar Shugaban tayi kukan cewa babu kayan aiki a asibitin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng