Za'a fara gina filayen kiwon Shanu cikin mako mai zuwa - Gwamnatin Tarayyah

Za'a fara gina filayen kiwon Shanu cikin mako mai zuwa - Gwamnatin Tarayyah

- Za'a fara aikin gina filayen kiwon shanu a jihohin da suka nuna sha'awa cikin shirin

- Gwamnatin Tarayyah ne ta sanar da hakan a ranar Juma'a 19 ga watan Janairu

- Gwamnatin Tarayyar kuma ta ce za ta yi hadin gwiwa tare da Ma'aikatar Binciken Dabbobi (NAPRI) domin ta taimaka wajen samar da abinci ga shanun

Gwamnatin Tarayyah ta ce za'a fara gudanar da ayyukan gina filayen kiwo a jihohin da suka nuna sha'awa a shirin cikin mako mai zuwa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ta ruwaito.

Ministan ayyukan noma da raya karkara, Cif Audu Ogbeh ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a 19 ga watan Janairu yayin da ya kai ziyara sashin Noma da Kimiyyar Dabobi na Jami'ar Ahmadu Bello da ke garin Zaria.

Za'a fara gina filayen kiwon Shanu a mako mai zuwa - Gwamnatin Tarayyah
Za'a fara gina filayen kiwon Shanu a mako mai zuwa - Gwamnatin Tarayyah

DUBA WANNAN: Matsin lambar da ake wa iyalan Jonathan ya isa haka: MASSOB ga Gwamnatin Tarayya

Ogbeh ya ce a wajen Taron Tattalin Arziki na kasa wanda aka gudanar ranar Alhamis ne aka kafa kwamiti na mutane 10 karkashin jagorancin Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da za su fara aiwatar da shirin, sauran mambobin kwamitin kuma gwamnoni ne guda 9.

Hakazalika, Ministan ya ce Gwamnatin Tarayyah za ta yi hadin gwiwa tare da Ma'aikatar Binciken Dabbobi na Kasa (NAPRI) domin ta taimaka wajen samar da abinci ga shanun.

A cewar Ministan, Kilace shanun a waje daya shine abin da ya fi dacewa domin yawo da shanun ya kan sa su wahala.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel