Wata sabuwa: Kudin cizo ya addabi fasinjan jirgi
Hukumar sufurin jiragen sama a kasar Ghana ta nuna kudirin daukar mataki a kan kamfanin jirgin saman British Airways sakamakon kudin cizo a wasu jiragen kamfanin.
Ministar sufurin jiragen sama na kasar Cecelia Dapaah ta ce kamfanin na iya karo da matsin lamba idan har bai dauki mataki ba a kan kudin cizo da aka ruwaito sun dabaibaye wasu jiragensa da ke jigila zuwa kasar.
Rahotanni daga Birtaniya sun ce kudin cizon da aka gani yana yawo a daya daga cikin jiragen na British Airways ya tilasta an dakatar da jirgin a tashar Heathrow a birnin Landon.
Kamfanin jirgin dai bai musanta kudin cizon ba kuma ya ce an canza jirgin wanda ya kamata ya tashi zuwa Accra kamar yadda BBC ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta wallafa bidiyon Sanatocin da suka soki gwamnatin tarayya
A cewar kamfanin wannan matsala ce da ba kasafai ake samu ba, kuma jami'ansa na kokarin magance matsalar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng