Ma'aikaciyar jinyan Asibiti ta hada baki da wata mata domin sayar da jariri
- An gurfanar da wasu mata biyu gaban kotu bisa laifin hada baki domin sayar da jariri
- Sai dai jaririn ya mutu bayan haiwawar sa
- Matan biyu sun musanta zargin da ake musu kuma Alkalin kotu ya dage sauraron karar zuwa 15 ga watan Febrairu 2018
A ranar Juma'a aka gurfanar da wata ma'aikaciyar jinyan Asibiti, Agulana Ndidi mai shekaru 33 da kuma wata Yakubu Lina mai shekaru 34 gaban wata kotun Majistare da ke Kaduna bisa laifin yunkurin sayar da jaririn.
Mai shigar da kara, Moses Leo ya fada wa kotu wani mai suna Komolafe Abiodun da ke zama a unguwar Malali ya tsegunta ma ofishin yan sandan CID a ranar 28 ga watan December amma daga baya aka mayar da binciken ofishin yan sanda na unguwar Barnawa.
KU KARANTA: Hukumar EFCC ta na binciken yadda $500m da Abacha ya sace su ka yi layar zana
Leo ya ce an kama wadanda ake tuhuma kuma an masu tambayoyi, kuma an gano cewar Ndidi ta hada baki da wani Yakubu Lina wanda ta haifa jariri kuma za ta sayar bayan haiwawan, sai dai jaririn ya mutu bayan haihuwa kuma an jefar da gawan a rafin da ke unguwar Narayi a Kaduna.
Sai mata biyun da ake tuhuma da laifin sun ce ba su aikata ba, kuma Alkalin na kotun Magistare, Mista Emmanuel Yusuf ya bayar da bellin su kan kudi naira dubu hamsin kowanen su, kotun kuma ta daga sauraren karar zuwa ranar 15 ga watan Febrairu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng