Rikicin makiyaya: Kungiyar Gwamnoni Najeriya ta kai ziyarar gani da ido jihar Benuwe

Rikicin makiyaya: Kungiyar Gwamnoni Najeriya ta kai ziyarar gani da ido jihar Benuwe

- Gwamnonin Najeriya sun je ta'aziyya jihar Benuwe

- Gwamnonin sun nuna alhininsu dangane da rikicin dake faruwa a jihar

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta aika ta kai ziyara jihar Benuwe da nufin jajanta ma gwamnan jihar, Samuel Ortom da sauran al’ummar jihar bisa ibtila’in daya afka musu, kamar yadda Legit.ng ta gano.

Wakilan kungiyar da suka kai wannan ziyarar sun hada da Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, na Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El-Rufai, sai kuma mataimakiyar gwamnan jihar Osun.

KU KARANTA: Mulki sai da lissafi, don haka ba’a raba ni da Kalkuleta – Inji Gwamnan jihar Jigawa

Gwanonin sun isa jihar ne a ranar Juma’a 19 ga watan Janairu, inda ta samu ganawa da gwamnan jihar, manyan jami’an gwamnatin da kuma jama’an jihar, inda suka mika sakon uwar kungiyarsu ga jama’an, tare da nuna alhinin halin da suka shiga.

Rikicin makiyaya: Kungiyar Gwamnoni Najeriya ta kai ziyarar gani da ido jihar Benuwe
Gwamnoni

Jihar Benuwe na daya daga cikin jihohin Najeriya dake fuskantar barazanar tsaro sakamakon rikici dake faruwa tsakanin Makiyaya da manoma, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, sauran jihohin da lamarin yayi Kamari sun hada da Taraba, Kaduna da Nassarawa.

Rikicin makiyaya: Kungiyar Gwamnoni Najeriya ta kai ziyarar gani da ido jihar Benuwe
Ziyarar

Rikicin makiyaya: Kungiyar Gwamnoni Najeriya ta kai ziyarar gani da ido jihar Benuwe
Jama'a

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng