Kotu ta jaddada umurnin kama Tsohon Gwamnan Jihar Enugu game da cuwa-cuwan N5.3bn

Kotu ta jaddada umurnin kama Tsohon Gwamnan Jihar Enugu game da cuwa-cuwan N5.3bn

- Babban Kotu a Abuja ta bayar da umurni a kama Chimaroke Nnamani, Tsohon Gwamnan Jihar Enugu

- Kotun ta bayar da umurnin a kama shi ne saboda bijirewa kiranyen ta da ya yi

- Sai dai kuma lauya mai kare shi ya yankan ma sa hanzari da kwanciyar asibit a kasar turai

A ranar Juma'a ne wata Babbar Kotu a Abuja ta yi watsi da rokon da Tsohon Gwamnan Jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, ya shigar na a kawar da umurnin kama shi da kotun ta yi. Alkali mai shari'a, Chuka Obiozor, shi ne ya yi watsi da wannan roko ya kuma jaddada lallai ne Nnamani ya bayyana a gaban Kotun.

Alkalin ya kuma yi watsi da jayayyar da Nnamani ya yi ta bakin lauyan sa, Mista Rickey Tarfa, na cewar kotu ta hana EFCC kama shi. Gabanin haka, Tarfa ya kuma yi jayayyar babu abun da za a tuhumi Nnamani da Odilin sa Sunday Anyaogu da shi.

Kotu ta jaddada umurnin kama Tsohon Gwamnan Jihar Enugu game da cuwacuwan N5.3bn
Kotu ta jaddada umurnin kama Tsohon Gwamnan Jihar Enugu game da cuwacuwan N5.3bn

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta na binciken yadda $500m da Abacha ya sace su ka yi layar zana

Akalla Alkalai 3 ne su ka gudanar da wannan shari'a gabanin ta koma hannun Alkali Obiozor a 4 ga watan Disamba na 2017. Sakamakon rashin bayyanar Nnamani da Anyaogu a gaban Alkalin ne ya sanya shi bayar da umurnin kama su.

Sai ga shi a ranar Juma'a, Anyaogu ya bayyana amma banda Nnamani, a inda Tarfa ya yankan ma sa hanzari da kwanciyar asibiti a kasar waje ya kuma gabatar da hoto don shaida. Shi kuwa lauyan EFCC mai shigar da kara, Kelvin Uzozie, ya yi jayayyar cewar tun 2014 a ke yada hoton a yanar gizo.

A halin yanzun dai Alkali Obiozor ya dage cigaba da shari'ar har zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu na wannan shekara. Ya dage shari'ar ne bisa rokon da Uzozie ya yi na a ba shi lokaci don zantawa da Hukumar ta EFCC game da yadda za su bullowa shari'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164