Dalilin da ya sa ba za a kara yin wahalar mai a Najeriya ba - inji Saraki
Shugaban majalisar tarayyar Najeriya sannan kuma shugaban majalisar dattijai duk dai ta Najeriya Dakta Bukola Saraki a jiya ya bayyana cewa zartar da kudurin dokar nan ta yadda za'a gyara bangaren harkallar man fetur ta Petroleum Industry Governance Bill, PIGB a turance da majalisar wakillai tayi zai kawo karshen wahalar mai.
Saraki ya bayyana hakan ne a jiya cikin wani sakon da ya aike ga 'yan Najeriya ta kafar sadarwar nan ta zamani ta Facebook jim kadan bayan zartar da dokar.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a wani labarin kuma, A jiya ne dai kungiyar malaman makarantar firamare dake a jihar Kaduna watau Nigeria Union of Teachers a turance ta sanar da matsayar janye yajin aikin da ta shiga na har sai- baba-ta-gani sannan ta kuma umurci dukkan 'ya'yan ta da su koma bakin aikin su.
Shugaban kungiyar dai reshen jihar mai suna Mista Audi Amba ne ya sanar da hakan jim kadan bayan kammala wani zama na gaggawa da suka yi da majalisar zartarwar jihar kan lamarin a garin Kaduna, babban birnin jihar.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng