Gwamnatin Tarayyah za ta samar wa mata da matasa 3m ayyukan yi
- Ma'aikatan ayyukan noma da raya karkara na kasa za ta samar daayyukan yi da dimbin mata da matasa a Najeriya
- Ma'aikatar ta ware jihohi 24 ne da za su amfana da shirin a karo na farko
- Ma'aikatan za ta samar wa wadanda za su amfana da shirin tallafi na kudi, kayayakin aiki da kuma hada su da yan kasuwa da za su siya kayan na su
Ma'aikatan ayyukan noma da raya karkara na kasa ta bada sanarwan cewa mata da matasa miliyan uku ne za su samu ayyukan yi karkashin wani shirin samar da ayyuka da inganta rayuwar iyalai ta hanyan aikin noma da akayi wa lakabi da (LIFE).
Mataimakin Direktan Ma'aikatar, Dacta Chinyere Ikechukwu-Eneh ne ta bayyana hakan yayin da ta ziyarci Ma'aikatar Aikin Gona na jihar Enugu a ranar Talata. Ta kara da cewa jihohi 24 ne za su amfana da shirin a karo na farko.
KU KARANTA: Matasan Kungiyar Ohanaeze Ndigbo sun umurci makiyaya su fice daga yankin Kudu
Ikechukuwu-Eneh ta kara da cewa matasa da mata yan shekaru 18 - 40 ne za su amfana da shirin, kuma manufan shirin shine bayar da gudunmawa wajen kawar da yunwa da kuma bunkasa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar samar da ayyuka da inganta ra'ayuwan al'umma.
Bugu da kari, ta ce za'a bukaci al'ummar da za su amfana da shirin su kafa kungiyoyin taimakon kai-da-kai, sannan a bukace su da su zabi irin sana'ar da suke sha'awan yi sannan a basu tallafin jari, kayayakin aiki kuma a sada su da kasuwannin da za su siya kayan na su.
Sakataren dindindin na ma'aikatan aikin gona na jihar ta Enugu, Mista Samuel Onyiaji ya bayyana shirin a matsayin abu mai mahimmanci, ya kuma yi kira ga wadanda za su amfana da shirin su nemi cikaken bayani kan shirin domin amfana sosai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng