2019 : Kashim Shettima yana kokwanton neman kujerar sanata
- Kashim Shettima yace wasu mambobin jam’iyyar APC suna hura masa wuta ya nemi kujeran sanata
- Shettima ya karyata jita jita zama mataimakin shugaban kasa da ake ta yadawa
Kwanakin kadan bayan ya fito a gidan Talabijin yace ba zai tsaya takara a zaben 2019 ba, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, yace wasu mambobin jam’iyyar APC suna hura masa wuta ya nemi kujeran sanata.
A wata hira da yayi da, Osasu Igbenidion, a gidan talabajin din AIT, Shettima ya fada mata cewa ba zai kara tsaya takara ba a lokacin da ta tambaye mai zai yi idan ya kamala wa’adin sa na gwamna.
Gwamnan Kashim Shettima ya ce zai je ya karo karatu idan ya sauka daga mulki, zai yi digiri a yaren Faransa.
KU KARANTA : Shittu ya zargi Ajimobi da nuna bangaranci da raba kawunan yan APC a jihar Oyo a wasikar da ya rubutawa Buhari
Kafin yanzu, ana ta yada jita-jita cewa, Kashima Shettima, zai ma mataimakin shugaban kasa idan Buhari ba zai tsaya takara ba a 2019.
Amma gwamnan ya karyata wannan zargi inda yace damuwar sa shine ya ga mutanen sa suna cikin zaman lafiya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng