Babu wanda za a ba tikitin Jam’iyya a sama – Inji APC
- APC tace babu ‘Dan takarar da za a kakabawa Jam’iyya a zabe
- Jam’iyyar Kasar tace za ta bi ka’ida wajen tsaida ‘Yan takara
- APC mai mulki tace babu maganar bada tikiti a sama ga wani
Yayin da lokaci ke ta tafiya, mun ji cewa APC mai mulki ta gargadi ‘Ya ‘yan Jam’iyyar game da zabe mai zuwa na 2019. Wani Shugaban Jam’iyyar ne yayi wannan gargadi kwanan nan nan a Jigawa.
Shugaban Jam’iyyar na Jihar Jigawa Alhaji Ado Sani Kiri ya bayyana wannan yayin da yake ganawa da manema labarai a babban birnin Jihar na Dutse. Jaridar Daily Post ta bada wannan rahoton ta bakin wani Hadimin Shugaban Jam’iyyar.
KU KARANTA: Masoya sun roki Kwankwaso ya hakura da takara a 2019
Alhaji Ado Sani Kiri yace kakaba ‘Dan takara ba tare da bin hanyoyin zabe ba ya sabawa ka’idar Jam’iyyar da kuma siyasar damukaradiyya. Shugaban Jam’iyyar yace ba za su saba wannan doka ba a duk kananan matakai har zuwa matsayin Jiha.
Shugaban APC na Jihar ya tabbatar da cewa Jam’iyyar mai mulki ta kowa ce don haka babu wanda za a hana takara a zaben 2019. Babban Shugaban na APC yace ko kadan ba za su yi gigin ba wanda bai ci zabe tikitin Jam’iyyar ba a zaben mai zuwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng