Dubi hotunan 'yan ta'adda da suka addabi matafiya a kan hanyar Suleja zuwa Bidda

Dubi hotunan 'yan ta'adda da suka addabi matafiya a kan hanyar Suleja zuwa Bidda

- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ci alwashin tabbatar da tsaro manyan titunan kasa

- Ta gabatar da wasu gungun 'yan ta'adda da suka dade suna addabar matafiya a kan hanyar Suleja zuwa Bidda

- Ta gargadi duk masu aikin ta'addanci da su canja hali tun kafin fadawa komar hukuma

A kokarin hukumar 'yan sandan Najeriya na tabbatar da tsaro a kan hanyoyin Najeriya, hukumar ta samu wata gagarumar nasara.

Hukumar ta 'yan sanda ta yi nasarar cafke gungun wasu 'yan ta'adda ne da suka dade suna addabar matafiya a kan hanyar Suleja zuwa Bidda da fashi da kuma satar mutane.

Dubi hotunan 'yan ta'adda da suka addabi matafiya a kan hanyar Suleja zuwa Bidda

'yan ta'adda da suka addabi matafiya a kan hanyar Suleja zuwa Bidda

Legit.ng Hausa ta samu bayanan cewar an kama da yawa daga cikin masu laifin ne bayan musayar wuta da jami'an 'yan sanda yayin da suke tsaka da aikata aiyukan ta'addanci. Kazalika hukumar 'yan sanda ta kubutar da wasu mutane uku da 'yan ta'addar ke rike da su, har ma sun yi ido hudu da iyalinsu.

DUBA WANNAN: Yaki da ta'addanci: Rundunar tsaro ta hadin gwuiwa ta gudanar da wani muhimmin taro a Maiduguri

A cewar kakakin hukumar 'yan sanda ta kasa, Jimoh Moshood, 'yan ta'addar sun amsa aikata laifukan da bakinsu.

Dubi hotunan 'yan ta'adda da suka addabi matafiya a kan hanyar Suleja zuwa Bidda

'yan ta'adda da suka addabi matafiya a kan hanyar Suleja zuwa Bidda

Hakazalika ya ce suna cigaba da bincike domin ganin cewar ragowar abokan 'yan ta'addar sun shigo hannu domin gurfanar da su gaban Shari'a.

Moshood ya ce duk wanda aka taba kwacewa mota ko aka taba sace masu mota da su je babban ofishin hukumar na jihar Naija domin duba motocin da hukumar ta kwato daga hannun 'yan ta'addan.

Bayan motoci, an samu makamai da tarin wasu kayan tsatsuba a wurin 'yan ta'addar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel