Da alamu Sarki Sanusi II ya fi Gwamnatin Jihar Taraba gaskiya a kan rikicin Mambila

Da alamu Sarki Sanusi II ya fi Gwamnatin Jihar Taraba gaskiya a kan rikicin Mambila

- Sarki Muhammadu Sanusi II yayi ikirarin an kashe Fulani sama da 800 a Taraba

- Gwamnatin Jihar ta karyata hakan duk da Sojojin kasar sun tabbatar da wannan

- Gwamnan Jihar ya bada umarni a saki masu laifin bayan rikicin da ya faru a bara

Mun samu labarin yadda Gwannan Jihar Taraba Darius Ishaku ya bada umarni a saki wadanda ake zargi da laifi a Jihar bayan rikicin da ya barke a Yankin Mambila da ke Karamar Hukumar Sardauna a bara.

Da alamu Sarki Sanusi II ya fi Gwamnatin Jihar Taraba gaskiya a kan rikicin Mambila
Sarkin Kano ya kai kukan Fulani wajen Gwamnatin Tarayya

Wasu takardu na wasika da su ka fito daga ofishin Kwamishinan shari'a na Jihar a bara sun nun yadda aka umarnin ayi maza a saki wadanda 'Yan Sanda su ka kama da laifin tada rikicin Mambila inda aka kashe Fulani rututu inji Jami’an tsaro na kasar.

KU KARANTA: PDP ta gargadi Gwamnonin APC game da zaben 2019

Da alamu Sarki Sanusi II ya fi Gwamnatin Jihar Taraba gaskiya a kan rikicin Mambila
Bangare na wasikar da Gwamnati ta aikawa Kwamishinan 'Yan Sanda

Kwamishinan ya bayyana cewa babu dalilin damke masu laifin tun da Gwamnantin Jihar ta nemi ayi bincike game da lamarin. Sarki Sanusi II ya bayyana cewa sai da aka kashe Fulani sama da 800 a karamar Hukumar Sardauna wanda Gwamnatin ta karyata.

A lokacin dai Rundunar Sojin kasar ta tabbatar da cewa an yi wa Fulani kisan gilla. Birgediya Janar Benjamin Ahanotu ya gane ma idanun sa inda yace ya ga ana kona yara da mata har da dabbobin su a gaban sa. Gwamnati dai ba su dauki wani mataki ba har yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng