Kotu ta zartar da hukuncin bulala shida a kan wasu mazaje hudu da laifin fyaɗe

Kotu ta zartar da hukuncin bulala shida a kan wasu mazaje hudu da laifin fyaɗe

A can jihar Katsina ne, wata kotu ta kama maza huɗu dumudumu da aikata laifin fyaɗe, inda ta zartar da hukuncin bulalai shida a kan kowanensu.

Waɗannan shu'umai da suka hadar da; Ahmed Lawal, Abdulmalik Usman, Adamu Khalid da kuma Abubakar Lawal, zasu fuskanci fushin kotu ne a sakamakon fyaɗe wasu 'yan mata biyu a ranar 20 ga watan Dasumba na shekarar da ta gabata.

Mazajen dai sun yi awon gaba ne da 'yan matan daga unguwarsu ta Kara, inda suka shilla wani ɓoyeyyen wuri kuma suka yiwa 'yan matan ta karfi domin biyan bukatunsu.

Fyaɗe

Fyaɗe

A yayin da mai shari'a Fadila Dikko ke zartar da hukunci ta bayyana cewa, kotu za tayi la'akari da neman rangwamin da masu laifin suka bukata duba da cewar wannan shine karo na farko da suka aikata laifi.

KARANTA KUMA: Badaƙalar N92m: Hukumar EFCC ta cafke ɗan tsohon gwamnan jihar Nasarawa

Legit.ng da sanadin jaridar Daily Trust ta fahimci cewa, baya ga bulalai shida, kotu ta baiwa masu laifin zaɓin zama a gidan kaso har na tsawon watanni biyar ko kuma kowanensu ya biya tarar naira dubu biyu tare da biyan diyyar naira dubu biyar na laifin da suka aikata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel