Wata mata ta sayar da yaro dan shekara 3 kan kudi N180,000 a Legas
- Ana tuhumar wasu mata biyu da laifin hadin baki don siyar da wani yaro mai shekaru 3
- Kamar yadda yar sanda mai shigar da kara ta fadawa kotu, Nduwe ne ta sato yaron daga wajen mahaifiyarsa domin ta sayar wa Nnabofe
- Wadanda ake tuhuma sun musanta aikata laifin, Alkali kuma ya dage sauraron karar zuwa 20 ga watan Febrairu
An gurfanar da wasu mata biyu, Helen Nduwe da Eucharia Nnabofe gaban Alkalin kotun Majistare da ke Ebute Meta na jihar Legas domin laifin yunkurin sayar da wani yaro mai shekaru 3 a duniya.
Jami'an yar sanda mai shigar da kara, Sajent Kehinde Omisakin ta fadawa kotu cewa wadanda ake tuhuma sun aikata laifin ne a ranar 31 ga watan Disamba a barikin yan sanda da ya ke Obalende a Legas.
DUBA WANNAN: Ba mu da filayen kiwon shanu, in ji Gwamnatin Jihar Taraba
Ta fadawa kotu cewa Nduwe ne da sato yaron mai suna Greatman Oche daga wajen mahaifiyarsa, sannan ita Nnabofe da saya yaron kan kudi N180,000, Laifin da ya sabawa sashi 227(a) (b) da sashi 411 na Dokar masu aikata laifi na shekarar 2015 na jihar Legas.
Sai dai matan biyu da ake tuhuma sun musanta aikata laifin. Alkalin kotun Mista Tajudeen Elias ya bayar da belin matan kan kudi N500,000 da kuma mutane biyu da za su tsaya musu.
Ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Febrairun 2018.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng