Ka yi murabus a matsayin ministan man fetur, jigon APC ga Buhari

Ka yi murabus a matsayin ministan man fetur, jigon APC ga Buhari

Wani jigon jam’iyyar APC kuma makusancin shugaban kasa, Alhaji Muhammad Ibrahim Daura, yayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari, da yayi murabus daga mukaminsa na ministan man fetur don mayar da hankali wajen ceto kasar.

A wani jawabi a Kaduna, a jiya, Daura yayi jayayya cewa ofishin shugaban kasa yana da matukar aiki sannan yana bukatar cikakkiyar kalawar shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda ya kawo cigaba ga kasar.

A cewarshi, mukamin ministan fetur abune mai matukar kulawa sannan kuma yana bukatar kulawar kwararru wadanda hankulansu baza suyi nesa ba daga aiki.

Ka yi murabus a matsayin ministan man fetur, jigon APC ga Buhari
Ka yi murabus a matsayin ministan man fetur, jigon APC ga Buhari

Abun bakin ciki ne cewa karamin ministan fetur, Ibe Kachikwu, wanda ya kasance lauya, maiyuwuwa baya da cikakkiyar masaniya kan kulawa da harkokin hukumar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisa na yau (hotuna)

Muna sane da cewa fiye da kashi 80 na kudin shigarmu tana zuwa ne daga fannin man fetur kuma idan bamu bada cikakkiyar kulawa bag a hukumar, kasar tana iya fadawa cikin rikici. Karamcin mai da kasar ke fuskanta a lokacin nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng