Yanzu Yanzu: An kwashi yan kallo a majalisa yayinda yan PDP suka tokare dan jam’iyyarsu daga komawa APC
An kwashi yan majalisar dattawa a ranar Laraba lokacin da sanatocin jam’iyyar Peoples’ Democratic Party suka hana dan jam’iyyarsu dake wakiltan Ebonyi ta kudu, Sonni Ogbuoji sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress, APC.
Mista Ogbuoji ya sanar da kudirinsa na sauya sheka daga PDP sakamakon rikicin dake cikin jam’iyyar.
Bayan sauraron kudirinsa, sauran sanatocin PDP suka katse masa hanzari sannan kuma a take majalisar ya kaure da hayaniya.
Hayaniyan ya dauki tsawon mintuna 10 yayinda sanatocin PDP suka tokare inda Mista Ogbuoji zai bi ya koma bangaren adawa.
KU KARANTA KUMA: Ku zamo masu hakuri a tsakaninku – Sakataren tarayya ga yan Najeriya
Daga baya sai Mista Ogbuoji ya janye kudirinsa domin ya faranta way an jam’iyyarsa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng