Jalingo: Gwamna Ishaku ya saka dokar ta baci a Taraba

Jalingo: Gwamna Ishaku ya saka dokar ta baci a Taraba

- Gwamna Ishaku na jihar Taraba ya saka dokar ta baci a garin Takum

- Wannan dokar ta biyo bayan kisan gillar da aka yi wa wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Takum

- Gwamna jihar ya yi Allah wadai da kisan kuma ya yi alkawalin tabbatar za a kama wadanda suka aikata laifin

Kisan gillar da aka yi wa wani dan majalisa mai wakiltar Takum a majalisar dokokin jihar Taraba, Yusha'i Ibi, yana neman haifar da tashin hankali a jihar sakamakon hakan ya sa gwamna Darius Ishaku ya sanya dokar hana fita a garin don kare duk wata rikicin da zai iya kunno kai.

Bugu da ƙari, jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an tura jami'an tsaro zuwa garin don taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya yayin da dokar hana fitar za ta ci gaba.

Rahoton ta bayyana cewa gwamnatin jihar ta kafa wannan matakan tsaron.

Jalingo: Gwamna Ishaku ya saka dokar ta baci a Taraba
Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku

An gano dan majalisar ya mutu, wanda ake zargin cewa wasu 'yan bindiga da suka sace shi suka kashe shi bayan sun karbi fansa N25 miliyan.

KU KARANTA: Wani shu'umin matsafi da ya kashe 'yan sanda biyu ya gamu da fushin sojojin Najeriya

Legit.ng ta fahimci cewa matasan Kuteb suna barazanar nuna rashin amincewar su da kisan killar da aka yi wa dan majalisar kuma sakamakon hakan ne gwamnatin jihar ta kafa wannan dokar.

Rahaton ta ci gaba da cewa an sace shi ne a gidan mahaifiyarsa a ranar 30 ga watan Disamban shekarar 2017 a Takum kuma daga bisani aka sami gawarsai a cikin gandun daji tsakanin iyakokin Taraba da Binuwai.

A halin yanzu ana zargin mambobin gungun masu garkuwa da mutane da kuma fashi da makami wadanda aka fi sani da Ghana daga jihar Binuwai suka aikata wannan kisan.

Gwamna Darius Ishaku ya yi Allah wadai da kisan Yusha'u inda ya yi alkawalin tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta gaggauta kama wadanda suka kashe shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng