Tsadar rayuwa da baƙin talauci ya sanya Magidanci hallaka iyalinsa gaba ɗaya

Tsadar rayuwa da baƙin talauci ya sanya Magidanci hallaka iyalinsa gaba ɗaya

Kimanin mutane biyu yan gida daya ne suka mutu, inda aka tsinci gawarsu a gidansu, wanda ya kone kurmus a yankin Weiteithie na jihar Kiambu, dake kasar Kenya.

Rahotanni sun tabbatar cewa Maigidan, mai suna Patrick Nderitu Karuiru ne ya aikata wannan aika aika, inda ya kashe matarsa, da yayansu guda uku dukkanins yan kasa da shekara 10, sa’annan ya banka ma gidan wuta, inda shi ma ya kone kurmus.

KU KARANTA: Da ɗumi ɗumi: Hukumar EFCC ta turke tsohon gwamnan jihar Filato a Abuja

Majiyar Legit.ng ta ruwaito makwabtansu ne suka fara ganin gobarar, inda suka rugo da nufin ceton su, amma shigarsu gidan keda wuya bayan sun kashe wutar, sai suka tarar da gawar iyalan a cikin uwardaka, yayin da suka tarar da gawar Maigidan a farfajiyar gidan.

Tsadar rayuwa da baƙin talauci ya sanya Magidanci hallaka iyalinsa gaba ɗaya, da shi kansa

Gidan

Bincike ya nuna yayan su uku sun mutu ne sakamakon shake wuyansu da mahaifin nasu yayi, tare da buga musu karfe, sa’nnan kuma yayi musu yankan rago, yayin da ya kashe matar ita ma ta hanyar buga mata karfe, wanda ya tarwatsa mata kai.

Daga karshe binciken yayi bayanin cewar bayan Maigidan ya halaka kowa ne, sai ya banka ma gidan wuta, inda shi kansa ya kashe kansa. Dai dai rahotanni a kasar Kenya sun danganta lamarin da bakin talauci da yayi ma Maigidan katutu, kuma babu sauki ko agaji dayake samu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel