Wani shu'umin matsafi da ya kashe 'yan sanda biyu ya gamu da fushin sojojin Najeriya
- Sojoji sun karya karyan tsafin wani mutum da ya kashe jami'an 'yan sanda
- Matsafin da abokansa sun addabi jama'ar jihar Akwa Ibom
- An samu makamai masu yawa a sansanin matsafan da aka kashe
Rundunar hukumar soji ta biyu a jihar Akwa Ibom ta ce ta kai wani samame a wata maboyar 'yan kungiyar asiri a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu, inda ta yi nasarar kashe shugaban kungiyar, Akaninyene Jumbo, bayan ta cin masa a iyakar jihohin Akwa Ibom da Abiya.
Mataimakin darektan yada labaran hukumar a jihar Akwa Ibom, Umar Shu'aib, ya sanar da haka ga manema labarai a jiya Talata, 16 ga watan Janairu.
"Dakarun sojin Najeriya, runduna ta biyu, sun yi nasarar kashe gawurtaccen dan kungiyar asiri, Akaninyene Jumbo da aka sani da Isopafit, a ranar 15 ga watan Janairu, a wani kauye dake kan iyakar jihar Akwa Ibom da Abiya. Mun yi nasarar gano inda matsafin ta hanyar amfani da wasu bayanan sirri," inji Shuaib.
KU KARANTA: Hukumar EFCC ta gurfanar da dan tsohon gwamna saboda cuwa-cuwan N92m
Isopafit fitacce ne a wajen aiyukan ta'addanci a karamar hukumar Ukanafun dake jihar Akwa Ibom.
Da yake karin bayani a kan aiyukan ta'addancin Isopafit, Shuaib ya kara da cewa "Ya taba jagorantar kisan wasu 'yan sandan Najeriya guda biyu da wani direban mota a ranar 17 ga watan Disamba, na shekarar da ta gabata. Kazalika ya taba kitsa kisan wata 'yar uwa ga wani kwamishina da karin wasu mutum biyu a garin Ikot Oko dake karamar hukumar Ukanafun a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2017."
Kafin gamuwa da ajalinsa, shugaban kungiyar asirin ya sha kaucewa kamun hukuma a lokuta da dama.
Bayan kashe Isopafit, dakarun sojin sun kai samame sansanin ragowar 'yan kungiyar sa dake kauyen Ikpe a karamar hukumar Etom Ekpo, tare da kashe wasu yaransa guda biyu, Aniebet Efiong Udoh da Thankgod Friday, yayin da wasu suka tsere da raunuka bayan musayar wuta.
An samu makamai a wurin 'yan ta'addar da suka hada bindigu, manya da kanana, da alburusai masu yawa.
An ajiye gawar 'yan ta'addar a dakin adana gawa na asibitin koyarwa dake Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng