Shugaba Buhari ya gaza kare rayukan mu inji Kiristocin Najeriya

Shugaba Buhari ya gaza kare rayukan mu inji Kiristocin Najeriya

- Kungiyar Kiristocin Najeriya sun nemi a sauke Shugaban ‘Yan Sanda

- C.A.N ta kuma nemi a canza kaf Kwamishinonin ‘Yan Sandan Kasar

- Kiristocin sun ce Shugaba Buhari ya gaza kare jinin su a cikin Najeriya

Mun samu labari cewa Kungiyar Kiristocin Najeriya watau CAN sun yi kira na musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya sauke Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya da Kwamishinonin ‘Yan Sanda daga mukamin su.

Shugaba Buhari ya gaza kare rayukan mu inji Kiristocin Najeriya
CAN ta nemi a canza IG na ‘Yan Sandan Najeriya
Asali: Facebook

Kungiyar ta CAN ta nemi ayi maza a tsige Sufeta-Janar na ‘Yan Sandan Kasar Ibrahim K. Idris saboda kashe-kashe da barnar da ke aukuwa a cikin Najeriya. CAN tace Gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza kare jinin ‘Yan Najeriya.

KU KARANTA: Kungiyar CAN ta karyata Sarkin Kano Sanusi II

Shugaba Buhari ya gaza kare rayukan mu inji Kiristocin Najeriya
Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya Ibrahim Idris

Sakataren Kungiyar na Kasa Dr. Musa Asake ne yayi wannan jawabi bayan wani taro da Kungiyar ta gabatar inda yace ta tabbata Jami’an tsaro sun gaza kare ‘Yan Kasar wanda hakan ya zama babban barazana ga Kirisocin Najeriya.

CAN ta zargi Sufetan ‘Yan Sandan Kasar da hura wutar fitina musamman a Yankin Kudancin Kaduna da Jihar Benuwe inda yake nuna bambanci wajen gudanar da binciken sa. Don haka ne CAN ta nemi ayi garambawul a harkar tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng