Tattalin arziki: Hannun jarin Najeriya yana cikin mafi Kasuwa a Duniya

Tattalin arziki: Hannun jarin Najeriya yana cikin mafi Kasuwa a Duniya

- Kasuwar hannun jarin Najeriya yayi kyau a wannan makon

- Hannun jarin Kamfanonin Dangote sun yi kasuwa a Duniya

- Abubuwa na ‘dan cigaba da mikewa a halin yanzu a Najeriya

Idan mu ka koma fannin tattali za a ji cewa kasuwar hannun jarin Najeriya ya motsa kwarai da gaske cikin ‘yan kwanaki kadan kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridun kasar nan da sama da Naira Biliyan 300.

Tattalin arziki: Hannun jarin Najeriya yana cikin mafi Kasuwa a Duniya
Kasuwar hannun jarin Najeriya ta motsa a Duniya

A cikin kusan mako guda kasuwar hannun jarin kasar ta karu da Naira Biliyan 335 wanda ya aka rufe kasuwar yanzu da hannun jarin sama da Naira Tiriliyan 15. Hannun jarin Kamfanin simintin Dangote da Bankin Zenith ne su ka sa aka samu wannan cigaba.

KU KARANTA: Shugaban Kasa Buhari zai ziyarci inda ake fama da kashe-kashe

Hannun jarin Kamfanin sukarin Dangote da kamfanonin giya na Kasar da kuma gidajen mai irin su MOBIL da FORTE ne su ka fi samun karbuwa a cikin kwanakin nan inji rahoton da mu ka samu daga Jaridar Daily Trust ya kasar nan a farkon makon yau.

Kwanaki kun ji cewa idan aka duba kasuwar hannun jari, to Tattalin arzikin Najeriya na cikin wadanda su ka motsa a shekara da ta wuce ta 2017 tare da Kasar Amurka da irin su Kasar Argentina. Kasashen Larabawa dai ba su ji dadi ba a shekarar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel