Anyi kira ga al'ummar Arewa suyi koyi da halaye irin na Tafawa Balewa

Anyi kira ga al'ummar Arewa suyi koyi da halaye irin na Tafawa Balewa

- Babban direktan hukumar (NNPC), Dacta Mai Kanti Baru ne ya yi wannan kiran

- Ya yi kiran ne taron wallafa wani litaffi kan rayuwar marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa

- Dacta Baru kuma ya yabawa mawallafin littafin Danlami Baban Takko

Babban direktan Hukamar albarkatun man fetur na kasa (NNPC) Dacta Maikanti ya yi kira ga al'ummar Arewa suyi koyi halayen zaman lafiya Primiyar Arewa na farko Sir Abubabar Tafawa Balewa domin samun dawamamen zaman lafiya da hadin kai a yankin da ka kasa baki daya.

Anyi kira ga 'yan Arewa suyi koyi da halayen Tafawa Balewa
Anyi kira ga 'yan Arewa suyi koyi da halayen Tafawa Balewa

Baru ya yi wannan kirar ne a ranar Litinin a taron wallafa wani littafi da marubuci Danlami Baban Takko ya rubuta a kan rayuwar Sir Abubakar Tafawa Balewa. An wallafa litaffin ne a rana mai kamar ranar da aka kashe shi

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta gurfanar da dan tsohon gwamna saboda cuwa-cuwan N92m

Baru wanda ya samu wakilcin babban direktan na sashin harkoki (EDS), Dacta Abdullahi Idris, Baru ya ce, "Abubakar Tafawa Balewa ya sadaukar da rayuwarsa wajen yima Najeriya hidima. Ya bada rayuwarsa domin hadin kan kasar nan. Ina son inyi kira ga yan Najeriya musamman matasa da su dage wajen sadaukar da rayuwar su wajen yima Najeriya hidima.

Dr Baru kuma ya yabawa mawalafin littafin da iyalan Sir Abubakar Tafawa Balewa bisa yadda suke tunatar da yan Najeriya irin kokarin da marigayin ya yi wajen ganin Najeriya ta zauna lafiya, ya kuma kara da cewa sai da zaman lafiya sannan Najeriya za ta cigaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164