Anyi girgizar kasar a birnin Madina
- Anyi girgizar kasa mai karfin 2.5 akan ma’aunin sikeli Ritcher a birnin Madina
- Rahotanni daga hukumomin kasa Saudiyya sun nuna girgizar kasar bata yi barna ba
Hukumar jan kwala (Civil Defence) na kasar Saudiyya ta sanar da cewa anyi girgizar kasa mai karfin 2.5 akan ma’aunin sikeli Ritcher a birnin Madina.
Girgizar kasar ya auku ne da misalin karfe 5.00pm Aggogon Najeriya a ranar Talata 16 ga watan Janairu ,2018.
A lokacin da aka samu wannan rahoton hukumomi kasar Saudiyya sun ce girgizar kasar bata yi barna ba kuma bata salwantar dar rai ko daya ba.
KU KARANTA : Shekau ya yi izgilanci ga iyayen 'yan matan Chibok a sabon faifan bidiyo
Hukumonin kasar sun ce girgizar ba mai karfe bane amma yana da hatsari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng