Barayin baturin motoci sun yi kamari a sakatariya na Katsina
- Wasu miyagu barayin baturi sun haddabi masu motoci a sakatariya na Katsina
- Wannan matsalar ta kai inda babu ranar da za ta wuce ba tare da labarin cewa batirin motar wani ya bace ba
- Wani ma'aikacin gidan rediyo na jihar ya ce kimanin baturin motoci 16 aka sace a watan jiya
Barayin baturin motoci a sakatariya na jihjar Katsina sun kara karuwa, wanda a halin yanzu ta haifar da rashin tabbas tsakanin ma'aikatan gwamnati da abokan ci gaba, rahoton jaridar Daily Trust.
Legit.ng ta tattaro cewa matsalar ta kai inda babu ranar da za ta wuce ba tare da labarin cewa batirin motar wani ya bace ba wanda kuma ke jawo fargaba ga masu motocin bayan ajiye motocin su.
Yawancin motocin da wannan lamarin ya shafa sune motoci na ma'aikatan gwamnati, motoci na gwamnati da kuma abokan cinikin ci gaba a jihar.
Saboda wannan matsalar masallatai daban-daban a cikin sakatariyar sun fara wayar da kai masu motoci a kan tsaro da kuma barayi su ji tsoron Allah kuma su nisanci wannan halin.
KU KARANTA: Jami’an tsaro na sirri sun diran ma wani Malami da yayi kira da a kada Buhari a 2019
Wani limami a ma'aikatar lafiya, Hussaini Mohammed, ya ce tawagar wasu ma’aikata sun taba kai karar al'amuran ga ofishin sakataren gwamnatin jihar don magance wannan lamarin.
A halin yanzu, wani ma'aikacin gidan rediyo na jihar wanda ya yi magana ba tare da izini ba ya ce kimanin motoci 16 da aka ajiye a gidan rediyon aka sace batirinsu a watan jiya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng