Iran ta shawarci kasashen Musulmi su rage dogaro da kasashen waje

Iran ta shawarci kasashen Musulmi su rage dogaro da kasashen waje

- Shugaban kasar Iran ya shawarci kasashen musulmai su rage dogaro da kasashen turawa

- Hassan Rouhani ya ce rashin dogaro da hadin kan kasashen musulmi kadai zai kawo karshen matsalolin da musulmai ke fuskanta a duniya

Shugaban kasar jamhuriyyar Musulunci na Iran, Hassan Rouhani, yayi kira ga hadin kan kasashen Musulmai tare da nesantar da kan su daga dogaro da taimakon kasashen turawa.

Hassan Rouhani ya bayyana hakane a lokacin bude taron hadin gwiwar ‘yan majalissar dokokin kungiyar gamayyar kasashen musulmi OIC a birnin Tehran

Iran ta shawarci kasashen Musulmi su rage dogaro da kasashen waje
Iran ta shawarci kasashen Musulmi su rage dogaro da kasashen waje

Rouhani yace hadin kan kasashen musulmi da rashin dogaro da kasashen waje ne kadai zai kawo karshen matsalolin da musulmai ke fuskanta a duniya.

KU KARANTA : Shekau ya yi izgilanci ga iyayen 'yan matan Chibok a sabon faifan bidiyo

Sai dai kuma ya kara da cewa, ba wai yana nufi su nesantar da kansu daga sauran kasashe bane, inda ya tabo batun yarjejeniyar nukiliyar kasar ta Iran da aka cimma a watan Yuli na 2015 wanda kuma shugaban Amirka ke ta baranar fitar da kasarsa daga yarjejeniyar.

Hukumomin kasar ta Iran dai na shan suka daga masu ra'ayin rikau na kasar kan yarjejeniyar nukiliyar da suka ce an yi ta ne kawai don amfanin kasashen yamma, alhali kuma Shugaba Rohani na ta kokarin janyo hankalin masu zuba jari na kasashen Turai da su zo domin zuba jari a kasarsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng