Shekau ya yi izgilanci ga iyayen 'yan matan Chibok a sabon faifan bidiyo
- Shekau ya saki sabon faifan bidiyo
- Ya ce iyayen 'yan matan Chibok surukansu ne
- Sama da 'yan matan Chibok 100 har yanzu na hannun kungiyar Boko Haram
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi gatsali ga iyayen 'yan matan Chibok a sabon faifan bidiyon da kungiyar ta fitar. Shekau ya ce iyayen 'yan matan Chibok su dauki mayakan kungiyar Boko Haram a matsayin surukansu.
Wani sabon faifan bidiyo da kungiyar Boko Haram ta saki a ranar litinin ya nuna wasu 'yan mata fiye da 12 da suka amsa cewar suna daga cikin ragowar 'yan matan Chibok da kungiyar ke rike da su. Da yawan 'yan matan sun bayyana dauke da jarirai a hannunsu, alamar dake nuni da cewar sun samu juna biyu har sun haihu.
Akwai akalla ragowar 'yan matan Chibok 100 da har yanzu ke hannun mayakan kungiyar Boko Haram.
Daya daga cikin 'yan matan da tayi magana a madadin ragowar, ta ce suna cikin koshin lafiya kuma basa son komawa wurin iyayensu. Mai maganar ta rufe fuskarta da nikaf, a saboda haka ba'a iya gane ta ba.
DUBA WANNAN: Hotuna daga bikin ranar tunawa da dakarun soji da suka kwanta dama
A cikin faifan bidiyon mai tsawon mintuna 36, Shekau, ya ce iyayen 'yan matan su dauke mayakan kungiyar boko haram a matsayin surukansu, domin suna auren 'ya'yansu ne. Shekau ya ce an nadi faifan bidiyon ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Janairu. Kazalika ya karyata rahoton hukumar soji da ya bayyana cewar yana fama da matsananciyar rashin lafiya. Shekau ya kara da cewa, 'yan matan Chibok 107 da kungiyar ta saki, ta sake su ne saboda sun ki komawa musulunci, yayin da wasu kuma sun ki yarda a aurar da su ga mayakan kungiyar.
Shugaban na kungiyar Boko Haram ya ce yana rike da karin wasu matan 'yan sanda guda 10 da ya kama su a hanyar Damboa zuwa Maiduguri bayan mayakan kungiyar sun yi wa ayarin sojin Najeriya kwanton bauna. Ya kara da cewar kokarin dakarun soji na kubutar da matan 'yan sandan bai samu nasara ba, yana mai bayyana cewar gwamnati ta yi asarar dakarun soji da makaman yaki a kokarin kubutar da matan.
Shekau ya ce kungiyar Boko Haram ba zata daina yaki da gwamnati ba, tare da daukar alhakin hare-haren bama-bamai da aka samu 'yan kwanakin nan.
An nuna matan 'yan sandan guda goma cikin hawaye a sabon faifan bidiyon.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng