Rundunar sojin Najeriya na shirin gina babban asibitin sojoji a jihar Sokoto - Tambuwal
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya yabi rundunar sojin Najeriya kan shirin gina babban asibitin sojoji a Sokoto domin ta kasance cibiyar martaba ga cututtuka dake da alaka da sojoji.
A wani jawabi da mai Magana da yawun Tambuwal, Imam Imam ya gabataar a ranar Talata, ya kwaso daga gwamnan inda yake cewa asibitin zata kasance na farko a kasar.
Tambuwal yace asibitin zai kasance cibiyar Karin ilimi tare dad akin gwaje-gwaje mai misali irin na cibiyar kiwon lafiya na Majalisan Dinkin Duniya.
Ya ce gwamnatin ta shirya samar da fili a harabar asibiti Murtala Muhammed Specialist na dan lokaci har zuwa tsawon lokacin da za’a karkare aiki a filinta na dindindin.
KU KARANTA KUMA: Ganduje ya zantar da hukunci kan dakatarwar da aka yi ma jarumar Rahama Sadau
Tambuwal ya ce har ila yau wassu jihohi sun bukaci da a kafa cibiyar a jihohinsu, amman jihar Sokoto ta kasance mafi karbabbiyar masauki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng