Gwamnatin Tarayya ta kashe N35bn wajen biyan kudaden ariya ga na ma'aikata
- Gwamnatin Tarayya ta fara biyan kudin ariya na karin girma ga hukumomi da ma'aikatun gwamnati
- Akanta Janar na kasa, Mista Ahmed Idris ne ya bayyana hakan bayan ya karbi rahoto daga kwamitin tantance ma'aikatu da hukumomin
- Akantan ya ce akwai sauran ma'aikatu da hukumomi da ake kan tantancewa kuma za su sami kudin nasu da zarar an tantance su
Gwamnatin Tarayya ta ware kudi naira biliyan 35 domin biyan kudaden ariya na karin girma da ma'aikatan gwamnati ke bi bashi a tsakanin shekarar 2011 - 2016. A halin yanzu, gwamnatin ta kashe sama da naira biliyan 30 kan ma'aikatu da hukumomin da aka tantance su kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga ofishin Akanta Janar na kasa ta ce.
Akanta Janar na kasa, Mista Ahmed Idris ya bada sanarwan ne bayan ya sami rahoto daga ofishin shugaban kwamitin tantance ma'aikatan da suka cacanta su karbi kudaden ariyar na karin girma, Mista Mohammed Kudu Usman.
DUBA WANNAN: Sojin Najeriya ta yi afuwa ga tubabun 'yan Boko Haram 244
Bayan ya nuna gamsuwarsa da aikin kwamitin, Akanta Janar na kasar ya ce biyan kudaden ariyar ya taimakawa ma'aikata wajen biyan bukatun su, ya kuma kara da cewa gwamnatin Tarayya ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen cika alkwawuran da ta dauka ga ma'aikatan.
A cewar Akanta Janar din, an ware kudi N8,249,083,829.50 domin biyan wadansu ma'aikatatu da hukumomi guda 68 da aka gama tantancewa kuma za'a fara biyan su nan ba da dadewa ba.
Daga karshe Mista Idris ya ce akwai wasu hukumomi da ma'aikatu da basu mika takardun neman hakokin nasu ba zuwa ga kwamitin tantance ariyar na karin girma, yace da zarar sun mika kuma an tantance su, za'a biya su na su kadaden.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng