Sojin Najeriya ta yi afuwa ga tubabun 'yan Boko Haram 244

Sojin Najeriya ta yi afuwa ga tubabun 'yan Boko Haram 244

- An saki tubabun mayakan kungiyar Boko Haram din ne domin murnar bukin tunawa da sojojin da suka riga mu gidan gaskiya

- Hukamar Sojin Najeriya ta ce tubabun 'yan Boko Haram din rabu da tsatsaurar ra'ayi da akidar da suke kai a da kuma za su iya komawa cikin al'umma yanzu

- A wurin taron, Gwamna Shettima a jihar Borno ya mika godiyar sa ga Hukumar Sojin bisa kokarin da sukeyi wajen samar da zaman lafiya da tsaro a yankin

A ranar Litinin ne Hukumar Sojin Najeriya ta mika tubabun mayakan Boko Haram sama da 244 zuwa ga Gwamnatin jihar Borno. Cikin wandanda aka yi wa afuwar, guda 118 maza ne, 56 mata ne sannan 19 matasa kuma da yara 51.

Kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicholas ne ya bayyana hakan a yayin da yake mika su ga Gwamna Kashim Shettima a makabartan Sojoji da ke Maimalari a Maiduguri.

Sojin Najeriya ta saki tubabun 'yan Boko Haram 244

Sojin Najeriya ta saki tubabun 'yan Boko Haram 244

Nicholas ya bayyana cewa yin afuwa ga mayankan kungiyar Boko Haram din da aka saki yana daya daga cikin abubuwan da Hukumar Sojin ta aikata domin murnar zagayowar ranar tuna wa da sojojin da suka riga mu gidan gaskiya.

DUBA WANNAN: Siyasar Kano: Ganduje ya kara gamuwa da wani babban cikas

Nicholas ya kara da cewa, "Shugaban hafsoshin sojin Najeriya, Laftanant Janar Tukur Buratai ne ya bada umurnin sakin tubabun mayakan Boko Haram din domin su koma ga iyalan su.

"Mayakan Boko Haram din da aka tsare sun tuna kuma sun rabu tsatsauran ra'ayi da akidar da suke da shi a baya, yanzu za su iya komawa cikin al'umma shi yasa muke mika su ga gwamnan jihar."

Gwamna Shettima ya yabawa Hukumar Sojin kan kokarin da ta keyi domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel