Jiga-jigan APC za su tattauna game da babban taron gangamin jam'iyyar su
Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki da suka hada da kwamitin gudanarwa na kasa, gwamnonin jam'iyyar da ma wasu manyan masu fada a ji a jam'iyyar za su yi wata tattaunawa a ranar Laraba, gobe kenan 17 ga watan Janairu a hedikwatar jam'iyyar dake a Abuja.
Jam'iyyar ta sanar da cewa wannan taron dai ana sa ran su tattauna ne game da babban taron gangamin jam'iyyar da ke tafe da kuma sauran shire-shiren jadawalin gudanar da jam'iyyar.
Legit.ng ta samu a wani labarin cewa Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a shekarun 2011 da kuma 2015 din da suka gabata watau Malam Salihu Sagir Takai ya kaddamar da wani kwamiti mai mutane biyar game da kudurin takarar ta sa a zaben 2019 mai zuwa.
Wannan kwamitin dai kamar yadda muka samu labari an kafa shi ne da zummar lalubo hanyoyi mafi sauki da dan takarar zai iya bi ya lashe zaben mai zuwa tare kuma da kula da sauran kungiyoyin dan takarar da za su fito.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng