Gwamnatin Tarayya ta maka Sanata Misau a Kotu kan yi wa ‘Yan Sanda sharri
- Kotu ta dage karar Gwamnatin Tarayya da Sanata Isa Hamma Misau
- Sanata Misau ya zargi ‘Yan Sanda da yin wasu ba daidai ba a Kasar
- Gwamnatin Tarayya tace sharri aka yi wa Sufetan ‘Yan Sandan na ta
Mun samu labari cewa an sa ranar da za a cigaba da shari’a tsakanin Sanatan Jihar Bauchi Isa Hamma Misau da Gwamnatin Tarayya inda aka zargin batanci ga Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya wannan watan.
Gwamnatin Tarayya ta maka Sanatan a Kotu ne bisa zargin sa da wasu laifuffuka da su ka hada da yi wa Sufeta Janar na ‘Yan Sadan Kasar Ibrahim K. Idris da kuma Hukumar ‘Yan Sanda da Tsohon IG na kasar Mike Okiro sharri.
Sanatan Bauchin ta tsakiya ya bayyana a Kotu tun bara inda ya musanya laifin kuma aka bada belin sa kan kudi Naira Miliyan 5. Daga baya ma dai Ministan shari’a yayi gyare-gyare kan laifuffukan da ake zargin Sanatan da su.
KU KARANTA: Sufetan 'Yan Sanda ya kai ziyara Jihar Benuwe
A karshen watan Nuwamban bara dai an yi zama wanda Lauyan da ke kare Sanatan watau Barista Joshua Musa yace karar da Gwamnatin ta kawo bai da inganci inda ya nemi Kotu ta hana masu karar sake daura wasu sababbin laifi.
A da dai mun ji cewa ana shirin sasantawa tsakanin Gwamnatin Tarayyar da Sanatan Kasar amma da alama ba a cin ma hakan ba. Yanzu haka dai Alkali Ishaq Bello ya ba masu kara damar daura wasu laifin inda ya daga kara zuwa karshen wata.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng