Likafa ta cigaba: El-Rufai ya rantsar da wasu sabbin jiga jigan jami’an gwamnatinsa

Likafa ta cigaba: El-Rufai ya rantsar da wasu sabbin jiga jigan jami’an gwamnatinsa

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya rantsar da sabbin kwamishinonin daya nada a kwanakin baya, inda ya mika musu shaidar rantsuwa a fadar gwamnatin jihar.

Daga cikin kwamishinonin akwai Ibrahm Hamza,kwamishinan ruwa, Ruth Geofrey Alkali, kwamishinan ciniki, yawon bude idanu da kasuwanci, Bilki Mary Luka Yusuf kwamishinan kula da kasha kashan kudaden gwamnati.

KU KARANTA: Yadda aka gudanar da bikin tunawa da ýan mazan jiya a jihar Kaduna

Likafa ta cigaba: El-Rufai ya rantsar da wasu sabbin jiga jigan jami’an gwamnatinsa

El-Rufai

Legit.ng ta ruwaito sauran sun hada da Daraktan hukumar kula da hanyoyi ta jiha, Muhammed Lawal Magaji, Shugaban gidan rediyon jihar Ibrahim Sama’ila Ahmed, shugaban hukumar kula da kayan gwamnati Musa Usman, shugaban hukumar bada agajin gaggawa Ben Kure sai kuma shugaban hukumar bada kananan basussuka, Kabir Ibrahim Goma.

Likafa ta cigaba: El-Rufai ya rantsar da wasu sabbin jiga jigan jami’an gwamnatinsa

Jiga jigan jami’an gwamnati

Bugu da kari gwamnan ya nada Hajiya Umma Aboki mukamin babbar mai bada shawara kan tattalin arziki da zuba jari, Bukus Banquo Audu babban mataimakiya kan al’amuran KADGIS, Nuhu Bello Yakubu, babban mataimaki ga gwamna kan kula da cigaba.

Likafa ta cigaba: El-Rufai ya rantsar da wasu sabbin jiga jigan jami’an gwamnatinsa

Jiga jigan jami’an gwamnati

Daga karshe gwamnan ya nada Ashiru Muhammad Haruna Zuntu da kuma Nasiru Zuntu a matsayin manyan mataimaka ga gwamnan kan watsa labaru da kuma tattara jama’a.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel