Sojoji biyu sun fadi a wajen faretin ranar rundunar sojoji
Sojoji biyu sun fadi a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu a wajen taron tunawa da ranar sojoji na 2018 wanda aka gudanar a filin Dr Alex Ekwueme Square, Awka, jihar Anambra.
Jami’an sojin biyu sun fadi ne yayinda suke gudanar da fareti.
Tawagar likitoci ciki harda kwamishinan lafiya na jihar Anambra, Dr Josephat Akabuike, sun ba wanda abun ya shafa kulawa kafin a dauke su zuwa asibiti domin basu cikakken kulawa.
Wani majiya na sojoji da ya nemi a sakaya sunansa ya fada wa majiyarmu cewa babu mamaki zafin rana ne ya hadda hakan.
KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Doguwa ya bukaci yan Najeriya da su marawa gwamnatin Buhari baya
A lokacin da aka tuntubi kwamishinan lafiya na jihar Anambra bai ce komai ba akan al’amarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng