Rundunar sojin sama ta kaddamar da wani gagarumin aiki a makarantar sojin sama na Uyo (hotuna)
- Rundunar sojin sama ta kaddamar da sababbin dakunan kwanan dalibai maza a makarantar ta dake Uyo
- An sadaukar da dakunan ne ga manyan daliban makarantar dake aji uku na babban sakandare
- Ana sa ran sabbin dakunan kwanan zai karfafawa kananan daliban gwaiwa wajen aiki da kwazo don samun daukaka zuwa manyan ajujuwa
A ranar 9 ga watan Janairu 2018, Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya kaddamar da sabbi dakunan kwanan dalibai maza a makarantar Air Force Comprehensive School (AFCS) Uyo.
An sadaukar da sabbin dakunan kwanan wanda injiniyoyin rundunan NAF fannin ayyuka ta gina ga jin dadin manyan dalibai na aji uku, na babban makarantar sakandare.
Ana sa ran sabbin dakunan kwanan zai karfafawa kananan daliban gwaiwa wajen aiki da kwazo don samun daukaka zuwa manyan ajujuwa.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamarwan, shugaban rundunan hafsan sojin sama ya yabi malamai da daliban AFCS Uyo kan abun burgewa da suka nuna a shekaru da suka gabata a sakamakon jarabawan manyan daliban makarantan sakandari (SSCE) hade da jarrabawar waje da gasanni.
Air Marshal Abubakar har ila yau ya shaida cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne sanadiyan kokarin da NAF ke yi wajen inganta ilimi a makarantunta.
KU KARANTA KUMA: Falana ya shawarci gwamnatin tarayya da ta saki El-Zakzaky da matarsa bayan ta tsare su ba bisa doka ba
Ya ce, “Muna nuna matukar godiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari kan samar da kayan aiki da muhalli da yayi don gudar da ingantacciyar tsarin aikin NAF”.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng