An raba ma mahaddatan Qur’ani kyautan Motoci da Babura a jihar Bauchi

An raba ma mahaddatan Qur’ani kyautan Motoci da Babura a jihar Bauchi

Zakarun gasar haddar Al’Qurani na jihar Bauchi sun samu tagomashi da suka hada da kyautukan motoci, Babura, Keke Napep da kuma sauran abubuwan alheri.

Daily Trust ta ruwaito an gudanar da bikin kamala gasar ne a garin Kirfi na jihar Bauchi, inda mahaddata 60 suka fafata a gasar, mata 20, maza 40, daga dukkanin kananan hukumomin jihar.

KU KARANTA: Ke Duniya: Karanta ta’asan da gungun yan fashi da makami suka tafka ma wata Tsohuwa

Zakaran gwajin dafin gasar shine Amir Yunus, wanda ya fito daga karamar hukumar Bauchi, sai kuma Nafisa Usman daga karamar hukumar Darazo ta zama kallabi tsakanin rawwuna. A biye dasu kuma akwai Nazib Ahmed daga Bogoro, sai kuma Amira Muhammed daga Katagum.

An raba ma mahaddatan Qur’ani kyautan Motoci da Babura a jihar Bauchi
Qur'ani

Majiyar Legit.ng ta jiyo shugaban kwamitin shirya musabakar, Mallam Zubairu Abubakar Madaki ya bayyana kimanin naira miliyan 53 ne gwamnatin jihar ta fitar don shirya musabaka a jihar da kasa bak daya, sa’annan ya kara da cewa za’a gudanar dana badi a Azare.

Shugaban ya gode ma uwargidar gwamnan jihar, Hadza Mohammed da babban alkalin kotun shari’ar Musulunci bias kyauytukan da suka baiwa gwarazan mahaddatan.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: