Kano: Ina daga cikin uban kungiyar Fulani Miyetti Allah - in ji sarki Sanusi
- Sarki Sanusi ya ce yana daga cikin uban kungiyar Fulani Miyetti Allah
- Sarkin Sakkwato da sarkin Katsina da sarkin Zazzau da kuma lamido na Adamawa suna daga cikin uban kungiyar
- Sanusi ya soki gwamnatin tarayya game da zargin harin da aka kai a kan makiyaya a jihar Taraba
Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, ya bayyana cewa yana daga cikin uban ƙungiyar Fulani wanda aka sani da Miyetti Allah (MACBAN).
Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, Sanusi ya ce kungiyar ba ta da alaka da tashin hankali a yanayin ta, kuma sarkin Sakkwato da sarkin Katsina da sarkin Zazzau da kuma lamido na Adamawa duk suna daga cikin uban kungiyar.
"Kamar yadda na fahimta lokacin da aka fara kafa kungiyar Miyetti Allah, sun bukaci wasu sarakunan Fulani su kasance uban kungiyar a matsayin su na sarakuna. Babbar uban kungiyar na farko shine Sultan Abubakar III kuma tun sa’a nan duk sarkin da aka nada zai maye gurbin magabata, irin su Dasuki da Maccido da kuma yanzu Saad Abubakar ", in ji shi.
"A mafi yawan abin da na sani, kungiyar Miyetti Allah ba ta taba shiga ayyukan tashin hankali ba, kuma kowane lokaci tana Allah wadai da tashin hankali a duk inda suka faru a fadin kasar kuma tana kira ga mambobinsa su kaurace wa tashin hankali”.
KU KARANTA: Na fara samun lafiya yanzu - Inji Sheikh Ibrahim Zakzaky
"Duk da haka, an kafa wannan kungiyar ne don kare hakkokin 'yancin makiyaya a matsayinsu na ‘yan Najeriya, ciki har da tsarin mulki wanda ta ba kowa ‘yancin motsawa da kuma mallakin dukiya da gudanar da kasuwanci".
Sarkin ya soki gwamnatin tarayya game da zargin harin da aka kai a kan makiyaya a jihar Taraba, inda kuma ya lura cewa kisan gillar da aka yi a yankin arewa ta tsakiya wasu ‘yan gida suka aikata.
A cewar Sanusi, kimanin mutane dari takwas ne 'yan tawayen Mabilla sun kashe a cikin ‘yan watannin da suka gabata, amma gwamnati ta kasa yin wani abu a kan lamarin duk da samun "bayanan bidiyo da na sauti na wasu manyan 'yan siyasa da ake tuhuma”.
"Babu abin da ya faru. Har ila yau, na tabbatar da cewa, hukumomi sun samu bayanan shaidan bidiyo da kuma na sauti na manyan 'yan siyasa a jihar Taraba, wadanda suke hannu a wannan kisan kare dangi. Babu wanda aka kama. Har ila yau an kashe Fulani da dama a Kajuru da Numan".
Har ila yau, sarkin ya soki dokar hana kiwo wanda gwamnatin jihar Binuwai ta sanya, ya ce yana iya haifar da rabuwa tsakanin mazauna da kuma makiyayan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng