La-liga: Abubuwa sun kara jagwalgwalewa Kungiyar Real Madrid

La-liga: Abubuwa sun kara jagwalgwalewa Kungiyar Real Madrid

– Abubuwa sun kara cabewa Kungiyar Real Madrid a bana

– Zakarun na bara su na bayan FC Barcelona da maki 16

– Villareal ta doke Real Madrid da ci daya mai ban haushi

A wannan makon an ga abin da ba a saba gani ba don kuwa Kungiyar Villareal ce ta zo har gida ta doke Real Madrid a Gasar La-liga. Real Madrid ta sha kashi ne da ci daya tak mai ban haushi.

La-liga: Abubuwa sun kara jagwalgwalewa Kungiyar Real Madrid

Villareal ta doke Zakarun bara har gida a Madrid

Real Madrid dai ta taka rawar gani a wasan sai dai daf da za a tashi ne ‘Yan wasan Villareal su ka arce su ka jefawa Kungiyar kwallo a raga. Wannan ne karo na farko da Villareal ta ci Real Madrid a gasar a gidan ta.

KU KARANTA: Kalaman Donald Trump sun bar baya da kura a Afrika

Kocin na Kungiyar Real Madrid Zidane ya ga ta kan sa bayan da ya sha kashi a wasan na wannan mako.Yanzu dai Barcelona ta ba Kungiyar maki har 16 a tebur inda kua maki daya tak ya raba Real da Villareal.

Wasu ma dai sun fara kiran a kori Kocin Kungiyar Zinedine Zidane. Zidane dai yace sun yi bakin kokarin su a wasan sai dai ci ne kurum bai zo ba sannan kuma sun gaza tare harin da Villareal su ka kai masu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel