Jam’iyyar PDP da APC sun sha kasa a zaben Jihar Anambra
Yanzu haka muna samun kishin-kishin din cewa Jam’iyyar APGA mai mulki a Jihar Anambra ta rabawa manyan Jam’iyyun Najeriya watau APC da PDP gardama a zaben Sanatan Jihar Anambra da aka yi.
Labari na zuwa mana cewa Jam’iyyar APGA na shirin lashe zaben Sanatan tsakiya na Jihar Anambra da aka sake yi a makon nan. ‘Dan takara Victor Umeh ne ke kan gaba inji Jaridar Premium Times da kuri’a sama da 64000.
Jama’a dai ko kadan ba su fito zaben ba, amma cikin kuri’u sama da 67000 da aka kada, ‘Dan takarar APGA yana da sama da 64, 879 yayin da Ministan kwadago na Gwamnatin Buhari watau Chris Ngige ya tashi da kuri’a 975.
KU KARANTA: An yi ca a kan Shugaba Buhari game da shirin sa na kara neman takara
Dama dai Ministan ya janye takarar kafin a kai ga kada kuri’a. PDP dai ta samu kuri’u 5 ne kacal a zaben da aka gudanar a kaf kananan Hukumomin Yankin. A baya dai Uche Ekwunife ce tayi nasara kafin Kotu ta soke zaben kwanaki.
Ga dai kuri’un nan amma da Hukumar INEC ba ta bayyana sakamakon ba tukun.
APGA - 64,879
APC - 975
PPA - 116
MPPP - 111
LP - 95
NCP - 72
ADC - 57
UPP - 55
GPN - 48 AA - 35 ACD
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng