Shugaban Sojojin saman Najeriya ya jinjinawa kokarin Shugaban kasa Buhari

Shugaban Sojojin saman Najeriya ya jinjinawa kokarin Shugaban kasa Buhari

– Rundunar Sojojin saman Najeriya ta gina wasu katafaren gidaje a Abuja

– Shugaban Hafsun Sojin yayi alkawari biyawa Sojojin kasar bukatun su

– Air Marshall Sadiqque Abubakar ya yabawa kokarin Shugaba Buhari

Shugaban Hafsun Sojojin saman Najeriya Air Marshall Sadiqque Abubakar ya kaddamar da wasu sababbin gidajen Sojoji a Birnin Tarayya Abuja a Ranar Juma’ar nan. A taron ya yabawa goyon bayan da su ka samu daga Shugaban Kasa Muhammad Buhari.

Shugaban Sojojin saman Najeriya ya jinjinawa kokarin Shugaban kasa Buhari

An ginawa Sojojin Najeriya da ke bakin aiki gidaje a Abuja

Marshal Sadique Abubakar yayi alkawarin ba Sojojin kasar na sama musamman wadanda ke filin daga duk wani taiamako da su ke bukata wajen shawo karshen ta’addanci a Najeriya wanda yace hakan ne za a kara masu kwarin gwiwa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun hallaka wani mutumi a Ibadan

Bayan kula da walwalan Sojojin, Hafsun Sojan yace za a rika ba Mayakan kayan aiki domin cigaba da aiki a filin daga. Air Vice Marshal Mahmoud Ahmed ne ya wakilci Shugaban Sojojin Air Marshal Abubakar a taron bude gidajen.

Rundunar Sojin sama na kasar ta tabbatar da cewa an sa sunan gidajen ne bayan wasu tsofaffin Sojojin su da su ka rasa kwanakin baya a wajen wani aiki watau Guruf kyaftin Usman Danliti Abubakar da kuma Marigayi Sajen Bolorunduro Raphel.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel