Na fara samun lafiya yanzu - Inji Sheikh Ibrahim Zakzaky
- Sheikh Zakzaky ya zanta da manema labarai karo na farko
- Babban Malamin na Shia'a yace yana ya fara samun lafiya
- Jagoran na Shia'a ya godewa irin addu'o'in da ake yi masa
A jiya ne Jagoran Kungiyar nan ta IMN ta Shia'a watau Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky ya zanta da manema labarai karo na farko tun bayan da aka tsare sa shekaru fiye da 2 da su ka wuce. An ga Malamin da dauri a wuyan sa.
Babban Shehin na Mabiya Shia'a ya bayyanawa 'Yan Jarida a Birnin Abuja cewa ta fara samun sauki kawo yanzu. Malamin addinin yace a farkon makon jiya, jikin na shi yayi tsanani, amma yanzu ya fara samun lafiya.
KU KARANTA: An kashe mutane 10 a Garin Kaduna kwanan nan
Malamin na Addinin Shia'a yace kuma wannan karo an ba sa dama ya ga Likitocin sa wanda a da can yace Likitocin Jamia'an tsaro ne ke duba sa. Daga baya dai Shehin ya tubure yace bai yarda kowa ya taba sa ba sai Likitan sa.
Sheikh Ibrahim Zakzaky ya godewa addu'o'in da Jama'a su ka rika yi masa a lokacin da yake tsare. Fiye da shekaru 2 kenan da Jamia'an tsaro su ka damke shi bayan wata takaddama tsakanin sa da Sojoji inda mabiyan sa da dama su ka mutu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng