Burina a duniya na auri Muhammadu Buhari - Jarumar Wasan Hausa

Burina a duniya na auri Muhammadu Buhari - Jarumar Wasan Hausa

- Jarumar wasan Hausa, Fati Shu'uma, ta ce burinta ta auri Buhari

- Ta ce Buhari kyakykyawa ne, son kowa

- Ta bukaci jama'a su taya ta da addu'a

Wata jarumar wasan Hausa, Fati Abubakar, da aka fi sani da fati Shu'uma ta ce bata da wani buri a duniya da ya wuce ta auri shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

" Wallahi Tallahi a rayuwata ban taba samun da namijin da ya shiga raina, ya kwamta min a rai kuma nake masifar son shi sannan nake burin auren shi, kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, sannan bani da buri da ya wuce na zama amaryar shi."

Burina a duniya na auri Muhammadu Buhari - Jarumar Wasan Hausa
Jarumar Wasan Hausa; Fati Shu'uma

Kalaman Jaruma Fati Shu'uma kenan kamar yadda ta furta yayin wata ganawa da ita da jaridar Blue Print ta yi a Kano, satin da ya gabata.

DUBA WANNAN: Hukumar tantance fina-finan Hausa ta janye dakatarwar da ta yiwa Rahama Sadau

Shu'uma ta kara da cewar 'duk inda ake neman namiji kyakykyawa to shugaba Buhari ya kai, gashi fari dogo mai wushirya sannan ga jarumta, wallahi duk macen da ta auri Buhari ta dace da miji, kuma hakika na kamu da son shi fiye da duk wani da namiji a duniyar nan, Allah ka sa in auri Buhari," inji Fati.

Fati ta cigaba da cewar "na san uwargidan shugaba Buhari, Aisha, kyakykyawar mace ce, amma duk da haka ina fatan karawa da ita wajen mallake mijinta, sannan ina rokon dukkan 'yan. Najeriya su tayani addu'a Allah ya cika min wannan burina nawa da nake kwana da shi ina tashi, sannan Wanda keda halin sanar da shugaba Buhari wannan buri nawa, don Allah ya taimaka min'.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng