Bana goyon bayan ware filayen kiwo na musamman ga makiyaya a Filato - Jonah Jang

Bana goyon bayan ware filayen kiwo na musamman ga makiyaya a Filato - Jonah Jang

- Jonah Jang yace al'ummar yankin sa basu goyon bayan kudirin gwamna Lalong na ware filayen kiwo na musamman ga makiyaya a jihar Filato

- Jang yace ya tattauna da al'ummar yankin nasa kuma sun ce baza su bayar da filayen da suka gada daga iyayen su domin a bawa makiyayan ba

- A ranar Alhamis ne, Gwamna Lalong ya shaida wa manema labarai kudirin nasa na gina filayen kiwon domin makiyaya wanda hakan yace zai magance rikicin tsakanin manoma da makiyayan

Tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Jonah Jang ya ce mutanen yankin sa ba su goyon bayan ware filayen kiwo na musamman domin makiyaya kamar yadda magajinsa, Gwamna Simon Lalong ya ke son yi.

Jang wanda ke wakiltan yankin Arewacin Filato a majalisar Dattawa ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, ya kara da cewa ya tuntubi al'ummar da ya ke wakilta kuma basu amince da hakan ba.

Jonah Jang yace baya goyon bayan ware filayen kiwo na musamman ga makiyaya a Filato
Jonah Jang yace baya goyon bayan ware filayen kiwo na musamman ga makiyaya a Filato

"Al'umma ta ba su goyon bayan gina wuraren kiwon, sun ce ba za su bada filayen da suka gada daga iyaye da kakanni domin gina wuraren kiwo ba," inji wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Jang, Mista Clinton Garba

DUBA WANNAN: An kama sojan gona da kayan hukumar FRSC dauke da katin shaidar aikin soja a Kano

A ranar Alhamis, Lalong ya shaida wa manema labarai cewa zai bullo da sabbin kebabun filayen kiwo a maimakon yin doka da za ta haramta kiwo a fili a jihar ta Filato.

Lalong yace ware filayen kiwon na musamman zai taimake wajen magance rikicin da ke faruwa tsakanin makiyaya da manoma tunda za'a kebe makiyayan ne a wasu filaye na musamman.

Sai dai Jang yace al'umman sa da aka ta kaiwa hare-hare tsawon shekaru da yawa basu shirya mika filayen su ga makiyaya da suke zargin sun ke kai mus hari ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164