Gombe: Gwamna Dankwambo ya karyata zargin cewa ya umarci a kama hadimin Atiku

Gombe: Gwamna Dankwambo ya karyata zargin cewa ya umarci a kama hadimin Atiku

- Gwamna Ibrahin Dankwambo ya karyata zargin cewa ya umarci a kama hadimin Atiku

- Kwamishinan yada labarai na jihar Gombe ya ce babu gaskiya a rahotannin, tamkar karya ce

- Kwamishinan ya bayyana cewa Dankwambo bai taba ba da umarnin kame Ibrahim Bage ba

Gwamnatin jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ya musanta zargin cewa ya umarci ‘yan sandan farar kaya wato DSS don kama Ibrahim Bage mai gudanar da ayyukan gidauniyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar (Atiku Care Foundation).

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, kwamishinan yada labarai na jihar, Umar Ahmed Nafada, ya ce babu wata gaskiya a rahotannin, cewa Dankwambo bai taba ba da umarnin kame Bage ba.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya umarce jami’an tsaro don kama Bage kuma ya masa gargadi a kan inganta zaben Atiku a matsayin shugaban kasa a jihar.

Gombe: Gwamna Dankwambo ya karyata zargin cewa ya umarci a kama hadimin Atiku
Gwamnatin jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo

Da yake jawabi ga 'yan jaridu a Gombe, Nafada ya ce gwamnan jihar ba taba tsoratar da kowa ba game da yi wa Atiku kamfe.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya halarci Sallar Juma'a tare da gwamnoni

Nafada ya bayyana rahotanni a matsayin karya cewa wasu mutane ne kawai wadanda ke neman haddasa rikici tsakanin gwamna da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Kamar yadda Nafada ya ce, "A koyaushe akwai kyakkyawan fahimta da kuma dangantaka tsakanin gwamna Dankwambo da Atiku Abubakar a kan sassan siyasa da na sirri.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng