Jerin manyan masu kudin Najeriya a shekarar 2018

Jerin manyan masu kudin Najeriya a shekarar 2018

- Mun kawo jerin manyan masu kudin da ake da su a Najeriya

- Aliko Dangote ya taka sama da Biliyan 12.1 a karshen 2018

- Adenuga da Folorunsho Alakija su na cikin Attajiran kasar

Dama can kun ji cewa a makon nan mu ka samu labari cewa Mujallar Forbes ta fitar da jerin masu kudi a Duniya da Afrika. Mun kawo jerin manyan Attajiran da ke Najeriya kawo yanzu:

Jerin manyan masu kudin Najeriya a shekarar 2018
Aliko Dangote na Najeriya yana cikin masu kudin Duniya

1. Aliko Dangote

Alhaji Aliko ‘Dangote na Najeriya shi ne Attajirin Najeriya da kuma kaf Nahiyar Afrika inda yanzu ya mallaki sama da Dala Biliyan 12. Shekara da shekaru kenan babu wanda ya kamo kafar babban ‘Dan kasuwar.

KU KARANTA: Mutane 3 da su ka fi kowa arziki a fadin Duniya

Jerin manyan masu kudin Najeriya a shekarar 2018
Alakija tana cikin manyan masu kudin Duniya

2. Mike Adenuga

Shugaban Kamfanin GLOBACOM watau Mike Adenuga shi ne na 2 a Najeriya kuma shi ne mutum na 5 a cikin masu kudin Afrika. Adenuga ya mallaki sama da Dala Biliyan 53.

3. Folorunsho Alakija

Alakija tana cikin matan da su ka fi arziki a Duniya. Ita ce kuma ta 15 a Nahiyar kuma tana bin bayan Mike Adenuga wajen kudi inda ta ba Biliyan 1.6 baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng