Baƙin haure sun hallaka masu garkuwa da mutane guda 4 a jihar Kano
Wasu mutane guda hudu da ake tsammanin masu garkuwa da mutane ne sun gamu da ajalinsu a hannun wasu kauraye a garin Doguwa na jihar Kano, inji rahoton Daily Trust.
Kaakakin rundunar Yansandan jihar, DSP Magaji Musa Majia ya tabbatar da kisan mutanen, inda yace an kashe su ne a ranar Alhamis 4 ga watan Janairu. Majia ya bayyana sunayen mamatan kamar haka: Basiru Musa, Dahiru Musa da da Muhammad Kiru.
KU KARANTA: 2040: Addinin Musulunci zai zamto na biyu mafi yawan mabiya a kasar Amurka
Majiyar Legit.ng ta bayyana cewar mafarautan sun tsallako karamar hukumar Doguwa ne daga garin Lere na jihar suna farautan masu garkuwan, inda suka yi kicibus dasu a garin, kuma suka aikatasu.
Haka zalika wani mazaunin garin Doguwa ya bayyana ma majiyar cewa kaurayen basu yi kasa a gwiwa ba, har sai da suka farauto wani mutumi mai suna Alhassan Mai Hali, inda nan ma suka kashe shi, suna zarginsa da taimaka ma barayin mutane, sai dai Mai Hali ya mutu ya bar mata uku da yaya 14.
“A yanzu haka akwai mutane da dama sun tsere daga gidajensu, musamman wadanda mafarautan ke zargin suna da hannu cikin ayyukan satar mutane tare da yin garkuwa da su.” Inji shi.
Daga karshe, Kaakakin yayi tir da wannan danyen aiki, kuma ya bada tabbacin kwamishinan yansandan jihar, Rabiu Yusuf ya aika da karin jami’an tsaro zuwa garin Doguwa don tabbatar da sun kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng