Rubutun da tayi a shafin ta na Facebook ya janyo mata daurin shekara daya

Rubutun da tayi a shafin ta na Facebook ya janyo mata daurin shekara daya

- Wata kotu ta yanke ma wata mata, Hin Vansreypov, yar kasar Cambodia hukuncin zaman gidan kaso na shekara daya

- An hanke mata hukuncin ne bisa kallaman da ta rubuta a shafin sada zumunta na facebook inda tace Farai ministan kasar ne ya kashe wani manazarcin siyasa Kem Ley

- An harbe Ham Ley har lahira ne a garin Phnom Penh a watan Yulin shekarar 2016 a wani shagon shan shayi kan zargin bashi

Wata kotu da ke garin Phnom Penh ta yanke wa wata mata hukuncin zaman shekara daya a gidan kaso bisa laifin kala wa Farai ministan Cambodia, Hun Sen, shari na daukan nauyin kisar wani mutum mai suna Kem Ley wanda ya shahara wajen sukan gwamnatin kasar.

Rubutun da tayi a shafin ta na Facebook ya janyo mata daurin shekara daya
Rubutun da tayi a shafin ta na Facebook ya janyo mata daurin shekara daya

An cafke matar mai suna Hin Vansreypov a garin Banteay Meanchey a ranar 10 ga watan Yuli bayan ta kira Hun Den da iyalan sa 'Masu aikata Kisa' a wani rubutu da tayi a shafin sada zumunta na Facebook yayin da ake bikin tunawa da ranar da aka kashe Ley.

DUBA WANNAN: Dubi wata karamar yarinya mai shudin idanu da ake zargi da maita

"Iyalan Hun Sen ne suka kashe Ley. Dukkan iyalan gidan Hun Sen suna da laifi cikin kisar." Kamar yadda ta matar mai shekaru 37 ta rubuta.

Kamar yadda jaridar Khmer Times ta ruwaito, Alkali Y Thavireak ya yanke mata hukuncin shekara daya a gidan kaso kuma ya umurce ta da biyan tara dalla 250.

Kafin rasuwar sa, Kem Ley mai nazarin harkokin siyasa ne kuma shine ya kafa wata jam'iyya na talakawa. An harbe Ham Ley ne a garin Phnom Penh a watan Yulin shekarar 2016 a wani shagon shan shayi kan zargin wata bashi da ake bin sa sai dai al'umma da dama a garin suna alakanta kisar na sa da siyasa

DUBA WANNAN:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164