Dubi wata karamar yarinya mai shudin idanu da ake zargi da maita
Ana zargin da maitan ne saboda launin kwayoyin idanun ta shudi ne a sabanin baki ko ruwan kasa mai duhu da aka saba gani a idanun mutane. A yayin da wasu ke zargin ta da maita, wasu kuma sun ce asiri akayi mata shiyasa idanun nata suka koma launin shudin.
Amma daga baya bincike ya nuna cewa launin idanun na ta ya canja ne saboda wata cuta da take fama dashi wanda a turence ake kira Waardenberg Syndrome (WS) wanda bai cika faruwa da al'umma sosai ba.
Wata mai taimakon al'umma, Afi Antonio ne ta fara lura da yarinyar saboda yadda mutane ke magana kan launin idanun na ta. Antonio tana rokon al'umma su taimaka da kudi domin ayi ma yarinyar magani.
DUBA WANNAN: Rikicin Benuwe: Idan gwamnati ba za ta iya kare mu, za mu kafa namu sojojin - Unongo
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng