Mai Kamfanin Microsoft Bill Gates, ya fi kowa dukiya a Duniya

Mai Kamfanin Microsoft Bill Gates, ya fi kowa dukiya a Duniya

Dama dazu kun ji cewa a Afrika babu wanda ya sha gaban Aliko Dangote, sannan a Duniya kuma babu masu kudin Bill Gates da kuma Warren Buffet da Jeff Bezos inda su ukun nan su ka mallaki sama da Dala Biliyan 230.

A makon nan mu ka samu labari cewa Mai Kamfanin nan na manhajar gafaka watau Microsoft, Mista Bill Gates ne ya fi kowa dukiya a Duniya. Mujallar Forbes ce ta bayyana wannan kwanan nan. Mun kawo sauran jerin sauran manyan Attajiran da ake da su:

Mai Kamfanin Microsoft Bill Gates, ya fi kowa dukiya a Duniya
Bill Gates da wani Attajirin Duniya Takwaran sa

1. Bill Gates

Idan ba ku manta ba tun shekaru 24 da suka wuce kusan kowace shekara sai ka ga sunan Bill Gates a cikin manyan Attajiran Duniya. A bana ma shi ne gaba inda ya tashi da sama da Dala Biliyan 86 a bara.

KU KARANTA: Aliko Dangote ne mai dukiyar Afrika na 2017 – Forbes

Mai Kamfanin Microsoft Bill Gates, ya fi kowa dukiya a Duniya
Babban 'Dan kasuwan Duniya Buffet ya kara arziki

2. Warren Buffet

Arzikin ‘Dan kasuwa Buffet ta habaka a karshen inda har ya zama na 2 a Duniya watau ya sha gaban Jeff Bezos da sama da Dala Biliyan 3. Buffet ya taki abin da ya haura Dala Biliyan 75 a Duniya.

3. Jeff Bezos

Mista Jeff Bezos ne wanda yake da Kamfanin nan na Amazon kuma tun shekarar 1998 ya shigo sahun Attajiran Duniya. A bara sai da ya doke Bill Gates na wani ‘dan lokaci amma yanzu an yi Dala Biliyan 72 nisa.

Dama dazu kun ji cewa a Afrika babu wanda ya sha gaban Aliko Dangote, sannan a Duniya kuma babu masu kudin Bill Gates da kuma Warren Buffet da Jeff Bezos inda su ukun nan su ka mallaki sama da Dala Biliyan 230.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng